The Spirit’s Voice

Daga nazarin da ya wuce mai taken “Hakkin Mai Bin Yesu.” Kalmomi na karshe sune:   “Wajibi ne mutane su yi karfin hali wajen kauracewa ga al’amuran ‘yan adam don mu iya gamsar da Ubangiji; don sai da bangaskiya kadai za mu gamshi Ubangiji (Ibran 11:6). Bautar ganin ido ta jawo wa bangaskiyar mutane mumunan hasara. Neman suna, girman kai da fahariya game da abin duniya sun raba mutane da bin maganar Littafi Mai Tsarki (Mat 23:5-12). Idan kuwa ba mu kaskantar da kai ba, ta yaya za a dogara ga bishewar Ubangiji ta karfin Ruhunsa? Sai mun yarda da kumamancinmu, sa’annan za mu yarda da ikon Ruhun Ubangiji da izawarsa.” 

Na gaskanta cewar wannan nazarin na dada karfafa bangaskiyar masu karatunmu, mussamman a fannin rayuwa cikin Ruhun Ubangiji. Muna kan nanata batun maida martabar sunan Ubangiji a cikin Ikilisiya a maimakon reni, kunya da abin dariya da ayyukan ‘masu bi’ suke jawo masa. Mutuntaka ita  ce babbar matsalar yawancin kirista a zamanin yau. Don iya bayyana wannan matsalar sosai, zan so in ba  da shaidar kaina a takaice:

Sunana Matthew Arin Adams. Ina da shekaru 64. Tun ina karami, na san iyaye na kirista ne; suna kuma aikin bishara. An koya mani maganar Ubangiji a Sonde Skul da makarantun da suka ilmantar da ni, daga Firamare har zuwa Makarantar Tauhidi. Amma a kashin gaskiya, na yi fama ko kuma gwagwarmaya da rayuwar ruhaniya ta kwarai da gasken gaske! Wannan famar ta yi karfi a lokacin da na kai aji uku a kolejin horon malanta a Bauchi (Teachers’ Training College) a shekara ta 1969. Da  ya  ke kiristancin bai sami karfi ko ikon cikar Ruhu Mai Tsarki da rayuwar bangaskiya ba, sai shaidan ya mori mutuntaka, sai na fara shaye-shaye; giya, sigari, tabar wiwi, kwaya da fasikanci.

Kamin nan, an rigaya an yi mani babtismar ruwa, ina cin jibin Ubangiji, ina rairawa da mawaka a cikin Ikilisiya (choir), ina kungiyoyin BB, matasa, bishara da sauransu. Me ya sa zan shiga cikin wannan halin idan a gaskiya ni mai bin Yesu ne? Gaskiyar ita ce, na  sami babtismar ruwa, amma ban sami ta Ruhu Mai Tsarki ba. Na ba  da gaskiya masu bi dayawa suna cikin wannan matsalar; an yi masu babtisma ta ruwa, suna cin jibin Ubangiji, suna ayyukan Ikilisiya dabam-dabam, har wadansu suna a matsayin dattawa, shugabannai, har ma pastoci da masu bishara; amma har yanzu ba su iya nasara a kan zunubi ba. Kirista dayawa ba  su san anfanin bangaskiyarsu ba ko kadan; idan ciwon kai ya same su, sai dai a nemi panadol ko aspirin, babu batun addu’ar bangaskiya don a  sami warkaswar ikon Ubangiji. Shi ya  sa Ikilisiyoyi dayawa suna da asibitoci da wuraren shan magani. Sai na tuna da ayyukan da Almasihu ya bar wa manzanninsa, su kuma suka bar wa Ikilisiyar da muke ciki yanzu. Yesun da muke bi bai aiki wani marar lafiya zuwa asibiti ko gidan magani ba; sai dai warkarwa kai tsaye. To, a ina ne muka sami batun dogara ga likitoci da shan magani a maimakon warkarwa ta wurin bangaskiya da bishewar ikon Ruhu Mai Tsarki?

Wannan da wasu damuwoyi ne na fuskanta a rayuwar kiristanci na tun ina matashi. Bin Yesunmu a lokacin ya kasance al’adar turawar da suka kawo mana ‘bishara.’ Me ya  sa  na fada haka? Me ya hana iyayenmu da shugabanai da pastocin da suka karbi wannan aikin daga garesu komawa ga Littafi Mai Tsarki don su koyi hidima irin ta Yesu Almasihu ba? Har yanzu, me ke hana wadannan Ikilisiyoyin yin karfi hali cikin bangaskiya da bishewar Ruhu Mai Tsarki don a koma ga koyaswar Almasihu a maimakon dogara ga ilimin mututaka ko kwaikwayon gudanar da al’amura irin ta duniya?

Na ci gaba cikin wannan rayuwar lalacewa fiye da shekaru uku; na kusan haukacewa. Da Ikilisiya ta yarda da mu’ujizai  kamar yadda Almasihu ya bar mana gurbi a cikin Matiyu 10:1-8; Markus 6:7; Luka 9:1-2, ai  da na sami kubuta daga wadannan ruhohin mulkin duhu da suka mallake ni a lokacin.

Amma godiya ta tabbata ga Ubangiji, ta wurin jinkansa da alherinsa, na sami kubuta sa’anda na sami saduwa da wadanda suka dauki Maganar Ubangiji Yesu da gaskiya, da aka yi mani addu’a, shike nan, sai na sami saki daga daurin shaidan! Daga wannan lokacin a 1973, a Lagos na sami ‘yanci daga shaye-shaye da dukan sauran zunuban da suka mallaki rayuwata. Na gode da ikon da ke cikin sunan Yesu da bishewar Ruhu Mai Tsarki. Nan take na sami marmarin yin aikin Ubangiji.

Amma fa har yanzu da sauran magana. Idan mutum ya sami kubuta daga mulkin duhu amma bai sami bishewa ta gari daga shugabancin Ikilisiyarsa ba, sai a shiga wata sabuwar matsala. To, inda na sake samun kai na ke nan. Ga rayuwa ta sauya zuwa babbar nasara, amma babu koyaswa da almajirci irin na Yesu, sai dai irin na darika. Ina daukar wannan matsalar mataki na biyu cikin rayuwar kirista. Na farkon ita  ce, ka tuba, ka yi babtismar ruwa, har ana ayyukan Ikilisiya, amma babu nasara da zunubi, shaidan da mutuwa! Mataki na biyu, an sami sabuwar rayuwar gaskiya, ga marmari ko sha’awar bauta wa Ubangiji, amma babu koyaswar gaskiya da almajirci na gari bisa koyaswar Littafi Mai Tsarki ta wurin bishewar Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. To yanzu sai yaya? Ga marmarin yin aikin Ubangiji, shine ‘Kiran Ubangiji’ a cikin rayuwar mutum, amma a cikin nema an kuce wa gaskiya?

Bisa ga tsarin darika, kafin a tabbatar da kiran Ubangiji a bisa rayuwar mutum, sai ka sami horaswa a makarantar Baibul, ko kuma na pastoci. Sai wannan ya zama wajibi a gareni. Sai na sami zuwa TCNN a 1976, da marmari a zuciyata! Na dauka wannan makarantar za ta zama mani kamar yanayin sama ne a nan duniya; amma, kash, abin takaici da ban tsoro, sai na tarar ba haka ya kasance ba. Me na gani?  (Zamu ci gaba a sharhi na gaba….)