The Spirit’s Voice

Yadda Shaidan ya ke hana Kirista karbar Baiwar Addu’a Cikin Harsuna

Addu’a cikin Harsuna.

 

Yadda shaidan yayi nasara wajen hana karbar baiwar Addu’a cikin Harsuna.

Shaidan ya yi nasara cikin yayata karyar hana Kirista samun Baiwar Harsuna. Akwai karairayi da yawan gaske da rashin fahimta a cikin ikilisiya game da wannan baiwar.

A takaice, bai dami Shaidan ba, idan Ikilisiya tana magana a kan baiwar, a yi nazari a kai, da yin mahawara a kai, a kuma yi tattaunawar rukunai a kai, amma ba zai taba yarda su karbi baiwar ba.

Ina amfanin sojar da ya ke da ilimi ko sani game da bindigogi, amma shi kansa ba shi da ko guda daya?

Rashin amfani da wannan Baiwar ta gurgunta Ikilisiya, wannan ne dalilin rashin ci gaba da girman masu ba da gaskiya da yawa kaiwa ga Ingantattun Baye-baye. Lokaci ya yi da zamu mori Baye-bayen da Ubangiji ya ba mu.

Idan kai Kirista wadda ba shi da baiwar Addu’a cikin Harsuna… Ya kamata ka samu.

Kada ka ci gaba da ba da hujjojin cewar ba ka bukatarta, ko kuma yadda ka nema amma kuma ba ka samu ba.
KAI DAI KA KARBI BAIWAR!

Idan ka rigaya ka karbi baiwar… Yi Amfani da ita. Ka Rura ko Zuga ta. Babu riba a ciki idan ta kwanta ko barci. Bari mu dubi wadansu KARAIRAYIN da suka hana Kirista karbar wannan baiwar.

Bari mu dubi wadansu karairayin da suka hana Kirista karbar wannan baiwar.

Karya Lamba ta 1

Wannan daga Ibilis ne, shi ne ya ke Magana ta gareka.

Babu wani misali a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewar baiwar harsuna na zuwa daga wurin Shaidan ne. Karanta 1Korintiyawa 12:3; Karanta 1Korintiyawa 14:14

Karya Lamba ta 2

Wai baiwar ba ta kowa da kowa ba ce.

Dalilin da karyata wannan tunanin shi ne kowane mutum a cikin ililisiyar farko ya karbi baiwar harsuna.

Bari mu dubi abin da Ayyukan Manzanni 2:1,4 ya ce, Karanta wadannan ayoyin.

Wani pasto abokin aikina yana hidima a taron falkaswa inda mutane wadanda yawansu ta kai 300 suka fito gaba mussamman don karbar wannan baiwar. Bayan ya yi addu’a, duka 300 din suka karbi baiwar. To, macece hujjar cewar wannan baiwar ba na kowa da kowa ba sai dai na wadansu kawai? Baiwar na nan don dukan wadda ke da bangaskiyar karba.
Karya Lamba ta 3: Na rigaya na yi kokari, bai yiwu ba, ba zan iya karba ba.
Yadda na sami fahimta game da al’amari, addu’a minti biyar bai isa don samun baiwar ba. Mai yiwuwa ne wadansu pastoci da suke da shafewa mai karfi suna iya addu’a har a sami baiwar da sauri, amma yadda na sani, dole ne mai nema ya dauki lokaci cikin addu’a da naciya kafin ya samu.

Koyaswa game da wannan baiwa zai zuga bangaskiyar mutane har su karba. Ya kan zama wajibi ka yi addu’a fiye da sa’a daya kafin ka karba. Don haka akwai bukatar hakuri cikin jira.